A gaskiya mu ba ƴan bangar siyasa bane, ka fito ka bamu haƙuri kawai, ko… Martanin Gungun matasa ga Gwamnan APC.

Matasa a ƙarƙashin inuwar APC ta jihar Borno dake kiran kansu da “Garkuwan matasan gamayyar jam’iyyu” sun yi kira ga gwamna Babagana Zulum da ya janye kalamansa inda ya kwatanta matasan jihar a matsayin masu haddasa rashin tsaro ta hanyar bangar siyasa kuma masu aikata laifuka gaba-gaɗi.

Matasan sun gargaɗi gwamnan da cewa in har bai janye kalaman nasa, anan gaba kaɗan ba za su tunatar masa akan yadda suka yi aiki tukuru don kawo shi kan gadon mulki.

class="has-text-align-justify">Da suke magana a wata hira da manema labarai a cibiyar ƴan jaridu a ranar Talata, mai magana da yawun ƙungiyar, Ibrahim Hassan ya ce:

“Haƙiƙa mun yi aiki tukuru don ganin mun kawo wannan gwamnati a kan mulki, sai dai Gwamna ya ce matasan ƙungiyar ECOMOG da Mohammed Yusuf ne suka haifar da rashin tsaro a Jihar.

A matsayin sa na uba gare mu, muna roƙonsa da ya janye wannan kalamai nasa gare mu. Domin mu ba ƴan ta’adda ko masu jagaliyanci da ake wa kallon bata gari bane ko kuma ƴan Boko Haram dake haddasa rashin tsaro a jahar mu mai albarka ba”.

Shugaban na ƙungiyar ya bayyana cewa ba sa jin daɗin halin marasa kirki dake a cikin su, shi ya sa suke ladabtar da su, yana mai jaddada cewa ba su ji daɗin kalaman da gwamnan ya yi na haɗa su da Boko Haram ba, amma a matsayin su na membobin jam’iyya masu bin doka, za su ci gaba da tallafawa gwamnati da jam’iyya gaba ɗaya har sai idan bai fito ya bada haƙurin ba.

APC

Da yake tabbatar da batun, wanda shima memba ne na matasan, Yakubu Dan Alhaji, ya ce:

“Haƙiƙa munyi yi aiki tuƙuru a baya don samun nasarar jam’iyyar tun daga farkon mulkin dimokuradiyya a 1999 Amma kuma sai ya saka mana da wannan kalamai, gaskiya bamu ji daɗi ba amma duk da haka muna roƙonsa da ya janye wannan magana sai dai idan yana ganin cewa shine ya kawo kansa kan mulki, muje zuwa.”

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *