An gurfanar da matashi a gaban Kotu sakamakon rubutun cin zarafi da yayi a Facebook tare da fassara Gwamna Ganduje da suna “Ɓarawon Kano”.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Kotun majistiri dake Anguwar Nomansland ta buƙaci wani matashi mai suna Ma’azu Magaji Danbala ya gurfana a gabanta sakamakon zarginsa da ake na ɓatawa Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje suna a shafin sada zumunta, Facebook.

Ana zargin matashin da ɓatawa Gwamnan suna tare da iyalansa wato Abdul’azin da Balaraba.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta wallafa, matashin an kama shi da laifin yin amfani da hoton Gwamnan haɗe da ƴaƴansa guda biyu tare da dangana su da kalmar “Ɓarayin Kano” wanda hakan ya saɓa da sashi na 97,114,391 da 399 a shari’ance.

Tun

da farko dai hukumar FIR ce ta turawa da matashin wasiƙar gayyata a rubuce, bisa ga zargin da ake masa na ɓatawa Gwamna Ganduje da iyalansa suna.

Babban mai Shari’a, Aminu Gabari ya umarci sashin binciken laifuka SCID da hukamar ƴan sandan Jihar Ƙano akan suyi bincike na tsanaki kafin kotu ta yanke shawarar bayarda belin matashin ko akasin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *