APC TSAGIN GANDUJE: Anyi musayar yawu mai zafi tsakanin Garo da Doguwa.

Akwai alamun cewa dake nuna ansoma samu rabuwar kai a tsagin APC na ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC a jihar Kano, biyo bayan arangama tsakanin manyan mutanensa guda biyu.

Mutanen biyu sune: Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, da kwamishinan ƙananan hukumomi,

Murtala Sule-Garo, inda mutanen biyu suka yi musayar kalamai masu zafi a wani shirin tallafi da Doguwa ya shirya a ƙaramar hukumar Tudun Wada.

class="wp-block-image size-full">

A shirin na tallafawar, an shaida rarraba injinan ɗinki na lantarki guda 500, injin ɗinki na hannu guda 500, tirela taki huɗu maƙile da takin zamani da motoci da babura da dama ga masu amfana daga mazabarsa, wanda aka gudanar ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Tudunwada ta jihar. A cikin jawabinsa a wurin taron, Sule-Garo, ya yi wa Doguwa “abin ba’a salon shaguɓe” cewa yana fatan tallafin da za’a bayar ya zama na gaskiya ne ba alƙawarin shafcin gizo ba.

Da alama waɗannan kalamai basu yiwa Doguwa daɗi ba, hakan yasa ya fusata nan take ya umarci masu taimaka masa da su kawo jakunkunan da ke ɗauke da zunzurutun kuɗi Naira na gugar naira har Miliyan 70, inda nan take ya jefar dasu a gaban matar Gwamnan Kano, Farfesa Hafsat Umar Ganduje, wacce ita ce babbar baƙuwa a wurin taron.

A wani abu mai kama da yunƙurin kwantar da hankalin Doguwa, uwargidan gwamnan ta ce tana da tabbacin Doguwa zai zama kakakin majalisar wakilai, inda ta yaba masa kan ɗimbin ƙoƙarin da yake yi na inganta rayuwar mazabarsa Ta ƙara da cewa ba za su bari wani ɗan siyasa ya dagula tsarin siyasar jihar ba.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *