Ba Na Goyon Bayan Yawan Ciyo Bashin Da Shugaba Buhari Yake Yi – Hon. Gudaji Kazaure.

Honourable Muhammadu Gudaji Kazaure Dan majalisar Tarayya daga Jihar Jigawa, mai wakiltar Roni, Yan kwashi, Guiwa, Kazaure ya ce ba ya goyon bayan yawan ciyo bashi da Shugaba Buhari yake ta yi daga kasashen waje.

Ya ce a matsayinsa na Dan Majalisa mai wakiltar Talakawan Najeriya gaba daya ya ce yana Shawartar Shugaba Buhari maimakon yayita ciyo bashi daga kasashen ketare gwara ya kafa wata hukumar da zata binciki wadanda suka sace kudaden kasarnan musamman a bangaren man fetur ayi duk ayyukan da za a yi dasu maimakon yawan ciyo bashin nan.

Hakanan

Gudaji Kazaure ya tabo bangaren yaki da cin hanci da Gwamnatin Buhari take ikirarin cewa tana yi, Gudaji Kazaure ya ce ana fadar ana yaki da cin hanci da rashawa ne kawai a iya baki amma babu a aikace, kamar yadda yake fada a cikin bidion nan a wata hira da yayi da ‘yan Jaridu Na Gidan Telebijin Na Liberty a Abuja.
https://www.jaridarmikiya.com/wp-content/uploads/2021/10/VID-20211009-WA0000.mp4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *