Babu wani nagari a Jam’iyyar APC, gungun ƴan rashawa ne a cikinta. ~Inji Sule Lamido

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma ginshiƙi a Jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido ya bayyana Jam’iyyar APC a matsayin matacciyar Jam’iyyar da bazata iya aiwatar da abin alkhairi ga ƴan Nigeria ba.

Lamido ya bayyana hakan ne a daren Jiya, yayin tattaunawa da wakilan Trust TV a shirin fagen siyasa.

Yayi zargin cewa dama can an ƙirkiri APC ne kawai domin karɓar madafun iko, amma Jam’iyyar bata da ƙwarewar tafiyar da mulki tare da dabarun kawo cigaba a Nigeria.

Sule Lamido, ya ƙara da cewa, “koda yaushe mahukuntan Jam’iyyar APC suna bayyana PDP a matsayin ƙazanta kuma a kullum ƙoƙarinsu shine su yaudari ƴan Jam’iyyar PDP domin su koma APC. Kuma kowa ya san cewa duk APC babu nagari, Jam’iyyar ƴan rashawa ce kawai.

Har’ilayau,

Sule Lamido ya kuma bayyana cewa PDP tana da damar taka rawa a zaɓen 2023 mai gabatowa.

A ƙarshe, Sule Lamdio ya bayyana PDP a matsayin Jam’iyya mai burin kawo sauyi a rayuwar ƴan Nigeria, kuma babban burin Jam’iyyar a halin yanzu shine ta kawo sauyi musamman la’akari da irin halin da aka shiga a Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *