Siyasa

Barkewar Rikici Ya Tilasta An Dage Zaben Jam’iyyar PDP A Jihar Neja.

Spread the love

An dage zaben jam’iyyar PDP da aka shirya gudanarwa yai Asabar a Jihar Neja.

An dage saboda rikici wanda ya dakatar da aikin zaben.

Wasu ‘yan daba da ake zargi da yin biyayya ga manyan masu takarar shugabancin a jihar biyu sun tsunduma cikin’ taron, wanda ya kai ga soke taron.

Kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa matsala ta fara ne lokacin da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Alhaji Baba Agaie, ya yi wa dandazon jami’an tsaro dauke da muggan makamai suka yi maza suka fita daga wurin taron.

NAN ta lura da cewa tun da misalin karfe 7 na safe, magoyan bayan ‘yan takarar biyu suka kwace sakatariyar PDP ta jihar ta da ke Western Bypass a Minna, duk kuwa da cewa akwai jami’an tsaro sosai.

An tattaro cewa wasu magoya bayan jam’iyyar sun buge Agaie da ake zargi da fito daga karamar hukumar Agaie.

Magoya bayan jam’iyyar sun zargi Agaie da yin zagon kasa ga bukatunsu na gamayya, suna masu zargin cewa ya hada kai da tsohon gwamna kuma jagoran jam’iyyar, Dakta Babangida Aliyu domin biyan wata bukata ta karan kansa.

Duk da haka, lokacin da hayaniyar ta lafa sai aka dakatar da zaben da za a gudanar, kwamitin zaben, karkashin jagorancin Malam Mohammed Imam daga Hedikwatar Jam’iyyar ta Kasa, sai da jami’an tsaro suka tursasa shi.

NAN ta ruwaito cewa bayan rudanin, kwamitin zaben ya fitar da sanarwa a Minna ranar Asabar dauke da sa hannun Imam.

A cewar Imam, saboda rashin tabbas na tsaro a sakatariyar PDP ta jihar da za a gudanar da zaben shugaban jam’iyyar ta jihar, wanda aka shirya gudanarwa a yau asabar 12 ga watan Satumba, da aka dage.

Ya ce an dage zaben ne bayan an yi kokarin ganin dubun dubatar magoya bayan jam’iyyar da sauran mutanen da suka taru a harabar wurin zaben sun watse kafin fara zaben.

Ya ce kwamitin zai gabatar da rahoto ga kwamitin aiki na kasa, NEC, wanda zai tantance matakin da za a bi na gaba kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

NAN ta ruwaito cewa manyan ‘yan takarar biyu sun hada da, Tanko Benji, shugaban jam’iyyar mai barin gado da ke neman wa’adi na biyu da kuma Mukhtar Ahmed.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button