Duk Jam’iyar data tsayar da ‘dan takara Kirista bayerabe a zaben 2023 tofa ta cire rai da samun ƙuri’un Muslimai Yarabawa ~MURIC

Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi (MURIC) ta bayyana ra’ayin bangaranci da fifikon kan dan takarar shugaban kasa zuwa ga Musulmin kabilar yuruba.

Kungiyar ta yi gargadin cewa duk jam’iyyar da ta zabi Kirista Kuma bayerabe a matsayin dan takararta na 2023 to ta manta da kuri’un Musilmin Cikin su kawai.

Babu wata jam’iyyar siyasa da za ta ce mana ba za su iya samun Musulmin kabilar yuruba da suka cancanta ba, ”in ji Farfesa Ishaq Akintola a ranar Litinin.

Sanarwar da Daraktan ya ce babu wani Musulmi bayerabe da ya taba mamaye gidan gwamnati ko a matsayin shugaban kasa ko mataimakinsa tun daga 1960.

MURIC

ta shawarci masu neman kujerar shugaban kasa da jam’iyyun da ke tsara dabaru don babban zabe mai zuwa da su saurari kiran nata.

Kungiyar ta yi ikirarin an hana su kusan dukkan ‘yancin walwalar jama’a, gami da shiga makarantu.

Akintola ya yi zargin cewa da yawa ba za su iya samun fasfo na kasa da kasa ba, lasisin tuki da katin rajistar masu jefa kuri’a saboda an nemi su cire hijabi domin Shiga Makarantu.

Ya ce makarantu suna wulakanta ɗaliban musulmai mata masu hijabi yayin da kotuna a Kudu maso Yammaci ke cike da ƙararraki “akan wannan jahilci na ɓatanci”.

Imaninmu ne cewa Musulman Yarbawa suna buƙatar ƙarfin tarayya don kawar ko aƙalla rage girman guguwar zalunci da Tsunami na ƙiyayya da Musulmi.

“Shugaba Musulmi Kuma bayerabe ne kawai wanda ya san abin da ke faruwa zai iya yin hakan da kyau shi ”, Akintola

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *