El Rufa’i Cikakken ‘dan dimokuradiyya ne Yana bawa kowa haqqin sa ~Sanata Uba sani.

A daidai Lokacin da Jam’iyar APC ke cigaba da zaben Shugabanni a matakin gundumomi da kananan hukumomi da zuwa matakin jiha a duk fa’din kasar Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya ya yabawa Gwamna El Rufa’i bisa tsarin tafiyar da Jam’iyar ta APC Mai Mulki a jihar musamman yadda Gwamna ya kammala tsarin Shugabancin Jam’iyar ba tare da wani tashin Hankali ba, Sanatan a sakonsa na yabo da ya aike ga Gwamnan Yana mai Cewa bari nayi anfani da wannan hanya ta musamman domin yaba wa gwamnan mu mai kaifin basira da hazaka, Mallam Nasir El-Rufai kan nasarar kammala Shirin Shugabancin gundumomi dana kananan hukumomi harzuwa matakin jiha, a jihar Kaduna tabbas ya nuna Karfin tsarin dimokradiyya Mai kyau Ya nuna cewa shi dan dimokuradiyya ne a cikin kalmansa na zahiri dana aika ce Ya nisanta kansa daga Shiga sabgar Shugabancin Jam’iya da na jiha Ya kyale masu ruwa da tsaki a kowane mataki su aiwatar da shirye -shiryen su a kokarin sa na bawa dimokradiyya damar bunƙasa a cikin jam’iyya, ya kafa ginshiƙi mai ƙarfi na wadatar dimokuraɗiyya a jiharmu Mai cike da kauna Inji Sanatan

Sanatan

yayi godiya ga masu ruwa da tsaki inda yake Cewa Ina kuma godiya ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar tamu ta Kaduna sakamakon nuna hadin kai wanda ba a saba gani ba da kuma yin amfani da zabin da aka cimma wajen cika mukaman jam’iyyar. Sadaukarwarsu da sasancin su ya nuna fifiko zuwa ga ra’ayin nasara fiye da bukatar kawuwan su, Jihar Kaduna ta Kasance abar kwatance ga wasu Jihohi dole muyi anfani da wannan dama domin raya wannan sabon tsari na dimokuradiyya domin hakan Ita ce hanyar samun nasara. Inji Sanata Uba Sani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *