Ganduje ya taimakeni ba zan iya kafirce masa nayi butulci ba ~Cewar Sanata Kabir Gaya.

Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Kabiru ya bayyana cewa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yi masa abinda ba zai iya yi masa butulci ba yanzu koma menene ya faru a tsakanin su..

Gaya ya ce ” Ganduje yayi rana a zaben 2019, dalilin sa na koma majalisa, ba zan iya yi masa butulci ba.

” Mun fara kungiyar tare da su Shekarau amma daga baya na zame kaina daga cikin su na fice daga wannan tafiya saboda na ga shirme ne rubuta irin wannan wasiƙa da muka yi wa gwamnan jiha sukutum.

Kira na gare su shine su zo su tsuguna da guiwowin su bibiyu su tuba so roki Ganduje, a sake yi musu wankan tsarki a dawo aci gaba da tafiyar tare. Sanata Kabir Gaya yayi wannan martani ne a wajen taron maida martani da aka gabatar a Gidan gwamnatin jihar ta kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *