GARGAƊI KO JAN KUNNE: Murtala abinda duk Allah ya baka muna murna, amma nan zaka zo kayi karatun jami’a , karatun gandujiyya, naja maka basin-mi-ara-alif-lallan hakuri — Alhassan Ado Doguwa zuwa ga Murtala Sulen Garo.

A wani gajeren faifan bidiyo wanda baifi daƙiƙa 30 ba, an hango tsohon bulaliyar majalisa kuma shugaban masu rinjaye na majalisa, watau Alhassan Ado Doguwa yana zabgawa Murtala Sulen Garo kalamai masu kama da barkwanci, amma ɗauke da saƙonni masu yawan gaske. Inda yake cewa:

“Ɗan ƙaramin ƙanina, kaima idan ka zama abinda muke fatan Allah yayi maka , To guna na zaka zo ka ɗauki karatu wallahi.

Kuma naji daɗi, iri nane na cikina, domin ni abokin Aminu Sule Garo ne da yayan sa.

class="has-text-align-justify">“Na isa nace Murtala inkagama abinda duk Allah ya baka muna murna, amma nan zaka zo kayi karatun jami’a , karatun gandujiyya, naja maka basin-mi-ara-alif-lallan hakuri.”.

Ga Faifan bidiyon:

https://www.jaridarmikiya.com/wp-content/uploads/2021/10/244609150_409952547498921_8851901696111300915_n-1.mp4

Alhassan Ado Doguwa na maida martani.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *