Ginin ‘daki a Kan kwalta ana musayar yawu tsakanin wasu matasa ‘yan jihar katsina bisa Rubutun ‘dan Jarida Ja’afar Ja’afar.

A Lokacin da yake maida martani ga wani matashi Mai suna Amb. Abdul Danja wanda yayi martani ga Ja’afar Ja’afar wani ‘dan Asalin jihar katsina Alh Sani Ahmad zangina yace ba karamin babban Abin kunya bane ace ‘dan Asalin jihar katsina ne zai maida martani ga Babban ‘dan jarida Ja’afar Ja’afar wai domin Kare Gwamnatin jihar katsina ƙarƙashin Jagororin Gwamna aminu Bello masari, amma dai zuwa gareka Malam Amb. Abdul Danja ka sani tabbas mu ‘yan Asalin jihar katsina masu kishin Jihar Katsina idan muka zura Ido, muka jira wai sai Jaafar – Jaafar ya maida maka martani Lallai ba muyi adalci ga kanmu ba.

Naji

takaici A Lokacin da nake bibiyar lamuran da Suka shafi matasan mu na jihar katsina yadda aka maida mana su zuwa ga mutuwar zuciya da maula da fadanci a wajen ‘yan siyasarmu na Jihar Katsina.

Da farko zai kyautu ka kasan cewa ba kafafen sada zumuntar zamani ke bayyana ayyukan Gwamna ba, Sanata ko ‘dan majalisa ba domin ayyukan ne da basu boyuwa kowa na gani a gari.

Misali ka dauki Ayyukan Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum na kwana 365 kawai, Zaka samu Ayyukan nasa sun zagaye kafafen sada zumuntar kuma ba Gwamnati bace take daukar nauyin masu tallatawar ba a.a Al’ummar gari ne ke Jin da’din Ayyukan kuma suke Alfahari dashi Hakan yasa suke saka Hotuna tare da rubuce-rubucen a shafukan su na sada zumuntar Zamani duk domin yabo ga Gwamnan.

Na biyu ka ‘daukko Sanata Babba Kaita mai wakiltar shiyyar Daura a majalisar dattijan Nageriya san nan kafadi tsakani da Allah a cikin Sanatocin da suke wakiltar jihar katsina Mutane uku shin waye mafi aiki da samarwa matasa guraban Ayyuka kyauta? Kai da kanka ko baka son Gaskiya ƙuri’arka Babba Kaita zaka bawa.

Batu Na uku ka kaddarama bamu da haraji kwata kwata a jihar katsina, shin lokacin gwamnatin marigayi Umar Musa Yar Adua da Gwamnatin Ibrahim Shema ka taba ganin inda ake tare ‘Yan achaba a tsakiyar hanya saboda haraji? Toh na gani a wannan gwamnatin musamman titin daya tashi daga kofar kwaya yabi gaban ATC zuwa National.

Abu na karshe shine, idan kace rashin ‘yan media ne yasa ba’a ganin ayyukan Alkhairi na Malam Aminu Bello Masari acikin jihar Katsina to amma ai yana da shafinsa na Kansa da Kuma shafi mai suna Katsina State government house, wanda ko yau an dora labarin Lokacin da Gwamna ke gabatar da kudrin kasafi ga majalisar (Presentation budget din 2022, me zai Hana baza’a saka sauran ba?

Karka manta duk irin ayyukan da Gwamna Ganduje keyi bai hana su Ja’afar Ja’afar su fadi gaskiya a kansa ba, shin meyasa ku baku son A fadi gaskiya akan Masari? wannan ‘dan karamin ‘dakin da ya jawo kace nace shin nawa ake bukata ne wai kwata-kwata kafin agama shi? da har zai ‘dauki shekaru ana abu ‘daya? Ko ‘dan majalisar Jiha zai iya yin wannan ‘dakin ba tare da ya jigata ba ballantana sanata ko gwamna.

Daga karshe zanyi anfani da wannan dama domin na bawa duk wani matashin mu na Jihar katsina Shawara akan muhimmancin sana’ar mai ‘dauke da kudrin dogaro dakai karku sake ku rai na sana’a komai kankantarta domin yawancin ‘yan siyasar mu suna nuna kaunar talakawa a daidai lokacin bukatar zabe ko wani taro na nuna yawan jama’ah..

Ja’afar Ja’afar mu ‘yan jihar katsina masu kishin ta Muna baka hakuri kaci gaba da fa’din Gaskiya akan Gwamnatin mu ta jihar katsina Munajin da’din Haka domin sai da Haka Jihar mu ta katsina zata cigaba..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *