Gwamna Wike Ya Taya Godwin Obaseki Da PDP Murna.

Gwamnan jihar Ribas kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na zaben gwamnan Edo, Gwamna Nyesom Wike, ya taya jam’iyyarsa ta PDP murna, lura da cewa sun cimma burinsu na kawo karshen ubangida, da farko a cikin jiharsa ta Ribas, yanzu kuma a Edo.

Kamar yadda sakamakon da INEC ta sanar kawo yanzu PDP ta bawa APC tazara mai yawa.

Wike ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter @NyesomWlKE, inda ya bayyana yadda sakamakon da INEC ta sanar kawo yanzu ya sanya PDP cikin kyakkyawan yanayi da sa ran samun nasarar, don haka ya kawo karshen bautar ubangida a siyasar Edo.

Wike

ya bayyana cewa burin jam’iyyarsa na kawo karshen kishin addini a jihar Edo ya biya, kamar yadda ya faru a jihar Ribas, ya kara da cewa, a siyasa, mulki da gaske na mutane ne.

Ya lura cewa musamman a yankin Neja Delta, iko na mutane ne, kuma an tabbatar da hakan tare da yadda sakamakon zaben Edo ya tafi.

Daga nan ya taya Gwamna Obaseki murnar sake zaben sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *