Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike yayi zargin cewa Shugaba Buhari ba shi da niyyar kwakwanta adalchi a zaɓen 2023.

Gwannan Jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bashi da niyyar kwakwanta adalchi a yayin zaben 2023 mai gabatowa.

Ya kuma zargi cewa babban muƙasudin da ya sanya Wakilan Jam’iyyar APC a majilisun ƙasa, suka ƙi amincewa da tsarin amfani da na’urar zamani domin tattara ƙuri’u, shine don sun shirya muƙarƙashiya tare da zaluntar ƴan Nigeria.

A cewar wani jawabi da ya fito ta hannun mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar ta Rivers a shafukan sada zumunta, mai suna Kelvin Ebiri, Wike ya bayyana haka ne yayin karɓar lambar yabo, a matsayin fitaccen Gwamna a shekarar 2020, wanda wata ƙungiya ta karrama yau Talata a garin Fatakwal na Jihar ta Rivers.

A

ƙarshe; Nyesom Wike ya ƙara da cewa, a halin yanzu mambobin APC a Majalisun ƙasa sun karkata ne wajen ganin an hana ƴan Nigeria damarsu ta zaɓar abinda suke muradi, shine dalilin da ya sanya suke sukar ƴan Majalisu waɗanda suka goyi bayan wannan sabon tsari.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *