Gwamnatin APC jahila ce, shekaru na 70, amma ba’a taba mummunar gwamnati irin ta Shugaba Buhari ba, |~ Inji Atiku

Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari da APC.

Atiku yace tun da aka haifesa bai taba ganin lokaci da al’umma suka fi kuka saboda tsananin wahala irin yanzu ba, rahoton PT.

Dan siyasan ya bayyana hakan ne jawabin da ya gabatar a taron gangamin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP dake gudana a dandalin Eagle Square dake birnin tarayya Abuja.

Atiku

yace: “Ba’a taba shiga mumunar hali irin wannan ba a kasar nan. shekaruna 70, kuma ban taba ganin lokaci sa ake shan bakar wahala, rashin tsaro da rashin hadin kai a Najeriya irin wannan ba.”

“Muna da daman gyara kasar nan da hada kan kasar nan. PDP ba ma’asumiyar jam’iyya bace, dukkanmu ba ma’asumai bane.”

Atiku yace jam’iyyar APC ta nunawa yan Najeriya karara cewa cike take da rashawa kuma ba zata itta mulkan kasar nan ba. “APC ta nuna cewa ba zata iya ba kuma mai rashawa ce.

Wajibi ne mu samar da kasar da zata daina nuna kabilanci kuma ta mayar da hankali kan iyawa.”

“Mutane sun kosa wannan kashe-kashe da sace-sacen kudin baitul mali da APC ke yi. Jahilar gwamnati da ta gaza komai yayinda yan bindiga suka mamaye titunanmu.”

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *