Jam’iyar Apc na so a hana Gwamna tambuwal karbo bashin biliyan 28.7bn.

Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen jihar Sokoto ta koka kan karuwar basussukan da jihar ke fuskanta.

Jam’iyyar adawar ta yi Allah-wadai da yadda gwamnatin Gwamna Aminu Tambuwal ta nemi a karbo sabon rancen kusan Naira biliyan 28.7 a kwanakin baya.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Isa Acida, ya bayyana haka ne a wata ganawa da manema labarai, a Sokoto, ranar Lahadi.

Ya bayyana neman rancen a matsayin wani mugun nufi da gwamna da gwamnatin sa ke yi na dora wa zuriyar da ba a haifa ba da basussukan da ba za a iya kwatanta su ba.

Acida

ya ce, “mu a jam’iyyar APC mun damu matuka da yadda aka bayyana cewa gwamnatin jihar Sokoto za ta sake karbar wani babban lamuni na Naira biliyan 28.7.

“Da wannan ci gaban, jihar Sokoto za ta zama jiha ta biyu mafi yawan bashi a Najeriya, sai Legas.

A jihar Sokoto ana ci gaba da fama da talauci da rancen da za a yi almubazzaranci a wasu sana’o’in da ba su da riba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *