Jam’iyyar APC tayi cinye duka a Jihar Filato, inda ta lashe zaɓe a ƙananan hukumomi 17 da kujerun kamsiloli 325.

Jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujeru a zaɓen Jihar Filato.

Bayan binciken ƙwaƙwaf, Jaridar Mikiya ta gano cewa Jam’iyyar APC a Jihar Filato tayi cinye duka, inda ta lashe kujerun ƙananan hukumomi 17 da kansiloli 325 a zaɓen da aka gudanar jiya Asabar.

A halin yanzu an gama bayyana sakamakon zaɓen, yayinda Gwamnan Jihar Barista Simon Bako Lalong ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda zaɓen ya gudana, duk da cewa dubban mutane a wasu runfunan zaɓen basu fito sun kaɗa kuri’unsu ba.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *