Karon farko za’ayi gadar Kasa ta kimanin zunzurutun Ku’di har sama da Bilyan biyar 5.8bn a jihar katsina.

Majalisar zartaswar jihar Katsina ta amince da bayar da kwangilar gina gadar kasa guda biyu (2) a cikin birnin Katsina.

Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na jihar Katsina, Alhaji Tasi’u Dahiru Dandagoro new ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Gadojin, kamar yadda majiyarmu ta Katsina Post ta ruwaito Cewa za a yi gadar ne a mahadar hanyoyin dake kofar Kwaya da kuma Kofar Kaura, dukkanin su a cikin birnin na Katsina.

Tasi’u

Dandagoro ya kara da cewa za’a kashe zunzurutun kudi har sama da Naira Biliyan biyar da miliyan dari takwas (N5.8bn) wajen yin gadojin kuma a ci watanni 12 kacal.

Da yake karin haske kan aikin, Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare, Alhaji Faruq Lawal Jobe yace aikin gadojin za’a yi shi ne da kudin bashin da gwamnatin zata ciwo ta kuma sanya a kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *