ku zo mu kubutar da Jam’iyar APC daga barazanar rushewa ~Jigon APC ya yi Kira.

Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Garus Gololo ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ce da su shiga cikin tattauna was da bangarori a cikin jam’iyyar sakamakon jihar tarnakin da aka samu bayan kammala Zaben Jam’iyar.

Gololo, wanda ya ce ya kamata Buni ya ceci jam’iyyar daga barazanar rushewa, ya kara da cewa rikicin barakar da ke cikin jam’iyyar ta reshen jihar Bauchi abin damuwa ne. A wani hira da manema labarai a Abuja, Gololo ya ce “ba zai yiwu Adamu Adamu wanda ya kasance karamin ministan ilimi kuma bai baiwa kowa daga jiharsa guraben karatu zai yi tunanin dora dan takara a jam’iyyar APC ta Bauchi.

Gololo

ya ce “Abin kawai yana nuna cewa shi ba ɗan siyasa ba ne kuma bai fahimci nufar aikin ba.” Jigon jam’iyyar ya kuma soki ministan wanda ya shawarce shi da kada ya yi takara da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

A cewar Gololo, “tun lokacin da Adamu ya hau kujerar mulki Adamu ya mayar da hankali ne kawai kan inganta rayuwar danginsa na kusa domin ko a mazabarsa ba shi da wani tasiri kai tsaye ko a matakin unguwa. Har ma ya sha kaye a zabe a hannun ‘yan adawa a mazabarsa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *