Kungiyar Agajin JIBWIS ta yabawa Sanata Uba sani kan Inganta rayuwar bil-adama.

Sanata Uba Sani ya Ga da Kungiyar ‘yan agajin Izalah Sanatan ne ya sanar da Hakan a shafinsa na yanar gizo Yana Cewa A yau ne na gana da ƙungiyoyin sa-kai a ci gaba da gudanar da shirye-shiryena da masu ruwa da tsaki a shiyyar Kaduna ta tsakiya. Na yi tarurruka daban-daban a karon Farko na gana da jami’an kungiyarJIBWIS ta kasa da jihar Kaduna, da kuma wasu zababbun gungun mutane masu kirkire-kirkire da dabaru wadanda suka tsara kungiya da manufar tallata ta a siyasance, da bayyana ayyukana da nasarorin da na samu da kuma gudanar da ayyukana yadda ya kamata. domin ganin APC ta ci gaba da samun nasarar zabuka masu gudana.

Sanatan

ya ce a tattaunawar da na yi da JIBWIS ta ta’allaka ne kan samar da ingantattun dabaru don inganta tasirinta wajen gudanar da ayyukanta na jin kai. Babbar kungiyar Agaji ta yabawa kokarina na samar da ababen more rayuwa da inganta rayuwar bil’adama a gundumar Kaduna ta tsakiya. Na ba su tabbacin ci gaba da goyon bayana.

Na umarci zababbun kungiyar da ke ci gaba da inganta ayyukana na zuwa ga talakawa tare da jan hankalin al’ummarmu musamman matasa da su ci gajiyar shirin rijistar masu kada kuri’a na ci gaba da karbar katin zabe na dindindin (PVC) domin Tabbatar da ‘yancin su na zabe a gaba. Na kuma ba su tabbacin goyon bayana gaba daya yayin da suke gyara dabarunsu da kuma kara kaimi wajen ci gaban manufofinmu na ci gaba da zabe. Inji Sanatan

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *