Matasa ku Guji karɓar wani mukami a karshen wannan Gwamnatin ta Ganduje ~Cewar muaz Magaji win-win

Tsohon Kwamishinan Ayyukan Ganduje muaz Magaji win-win ya Fadi wannan magana ne a shafinsa na Facebook inda yake Cewa To ai shawara ce…Wai wani yana kalubalanta na cewa ni me yasa na karbi appointment a gwabnatin Yayana? Ma’ana Gwamnatin Ganduje) Na ce masa , na farko dai na commissioner a second term ne muka zo gaba gadi dmin haska wa Baba matsalar gwabnatin da kuma tayashi aikin barin tarihi…ba aika aika ba…Na biyu kuma wato aikin AKK, aikin na da mahimmancin gaske ga Kano amma in ba a shigo da aika aika ba shima..to duk dai sai tarihi.
Alhamdulillah

ko su ma da kandy sai da sukai mana hassada kan samun shedar iya aiki cikin kankanen lokaci, abin ya dame su kwarai …suke son bata mana suna don hassada. Kuma sannan da kansu suka bada shedar bama biyayya akan aika aika…shine ai insubordination din da suke magana.

A Karshe muaz Magaji ya Kara da Cewa ina bawa ingantattun Matasa shawarar su yi hakuri, su daure su guji karbar appointment a karshen gwabnatin Yayan mu….domin masu hikima sunce…
A good name is better than gold and silver…
Su jira, tun da gwabnatin a gargara ta ke..saura kiris..

A watannin bayane muaz yayi barin zance Kan a Lokacin rasuwar Shugaban ma’aikatan Fadar Gwamnatin fadar Shugaban Kasa Abba kyari haka Kuma Tsohon Kwamishinan Ayyukan ya Saba ire iren wannan Maganganu a Kan Gwamnatin Ganduje Lamarin da ya jawo tsigeshi amatsayin Kwamishina da Kuma Shugaban kwamitin kafa bututun iskar gas na jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *