Matashi ɗan shekara 25, mai suna Muhammed Kadade ya zama Shugaban matasa na ƙasa ƙarkashin tutar Jam’iyyar PDP.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Matashin mai suna Muhammed Kadade Suleiman ya zama shugaban matasan ne bayan da aka gudanar da zaɓen cikin gida ƙarƙashin tutar Jam’iyyar PDP.

A jiya ne dai Jam’iyyar ta PDP ta gudanar da gangamin taro na ƙasa a filin Eagle Square dake babban birnin tarayya Abuja.

Muhammed Kadade, mai shekaru 25 kacal a Duniya haifaffen Jihar Kaduna ne dake Arewa maso yammacin Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *