Nayi alƙawarin gyara Nigeria cikin kwanaki 365 kacal. ~Inji Gwamna Yahaya Bello

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Duk da irin matsalolin tsaro, cin hanci da rashawa da suka addabi Nigeria; a gefe guda Gwamnan Jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello yayi alƙawarin gyara Nigeria a cikin kwanaki 365 idan aka bashi dama ya zama Shugaban ƙasa.

Bello ya bayyana hakan ne a ayau Litinin yayin ƙaddamar da jawabi a wani taro mai taken “Magance matsaloli” karo na 17 da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya bayyana cewa, bazai wuce kwanaki 365 ba zai gyara Nigeria ta kowanne fanni musamman ɓangaren tsaro.

Gwamna Yahaya Bello ya kasance ɗaya daga cikin matasa a Nigeria waɗanda suka nuna sha’awar tsayawa takarar Shugabancin ƙasar.

class="wp-block-gallery columns-1 is-cropped">

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *