Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, |~ Cewar Doyin Okupe

Tsohon babban hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Dr Doyin Okupe ya yi kira ga gwamnatin tarayya a kan sakin Nnamdi Kanu.

Ya bukaci gwamnati ta saki Kanu ko za a kawo karshen tashin hankali da rikicin da ke barkewa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

A cewar sa, sakin shugaban IPOB din ya fi muhimmanci a kan zaben gwamnan jihar Anambra da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Tsohon hadimin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilin Punch a Abuja yayin wani taron gangamin jam’iyyar PDP.

Daga

Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *