RIKICIN APC A KANO: Babu sanya hannunmu a harin da matasa suka kai ofishin yaƙin neman zaɓen Barau. ~A cewar APC ɓangaren Gwamna Ganduje

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ɓangaren Gwamna Ganduje ta musanta zargin cewa akwai hannunsu a cikin harin da wasu matasa suka kai ofishin yaƙin neman zaɓen Sanata Barau Jibrin (Maliya).

A ranar Alhamis ne dai wasu matasa suka kai hari ofishin na Sanata Barau, tare da farfasa waɗansu abubuwan da ƙone-ƙone.

APC ɓangaren G-7 wadda Sanata Ibrahim Shekarau yake Jagoranta sun shigar da ƙara ta inda suke zargin waɗansu daga cikin na bayan Ganduje da kitsa harin da aka kai.

Bayan

wannan shigar da ƙara ne, Jami’in hulɗa da Jama’a na Jam’iyyar APC wato Ahmed S. Aruwa ya bayyana zargin da ake yima Jiga-Jigan APC ɓangaren Gwamna Ganduje a matsayin mara tushe da kuma wani shiri ko ƙoƙarin ɓata musu suna a idanun Duniya.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta wallafa; Ahmed ya ƙara da cewa, harin da wasu mutane suke zargin ɓangare guda ne suka kai, yanzu ya zama ruwan dare a siyasar Nigeria. Kuma APC ɓangaren Gwamna Ganduje mutane ne masu bin dokar ƙasa don haka babu yadda zasu iya kitsa ayyukan ta’addanci.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *