Shuwagabannin Nigeria musamman na Arewa basu da cikakken ilimi a ɓangaren yadda ake Shugabanci. ~A cewar Farfesa Jega

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

n Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa wato INEC, Farfesa Attahiru Jega ya laburta cewa Shuwagabannin Nigeria basu da ilimi da cancantar da za’a kira su cikakkun Jagorori.

Ya bayyana hakan ne yau Litinin a loƙacinda yake gabatar da jawabi na musamman yayin wani taro da ƙungiyar ɗaliban Arewa ta gabatar. Ya kuma alaƙanta rashin tsaro tare da karyewar tattalin arƙizi a sakamakon rashin Shugabanci nagari.

Farfesa Jega, wanda shine Shugaban taron, ya ƙara da cewa “talauchi, rashin aikinyi ga matasa, auren wuri, rashin wadatattun cibiyoyin kiwon lafiya da kuma rashin tsaron da ya addabi Arewacin Nigeria a matsayin rashin iya jagoranci.

Mafi

akasarin waɗannan matsaloli da ire-iren annobar da ake fama da ita a Nigeria daga yankin Arewa suke fara wanzuwa.

A ƙarshe, Jega ya bayyana cewa Arewa babu Shuwagabannin da za’a kalla ayi alfahari da su. Jagororin Arewa mutane ne waɗanda basu da kishin al’ummar da suke wakilta sai son kawunansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *