WATA SABUWA: Gwamna Ganduje yayi kakkausar suka ga Sanata Ibrahim Shekarau, Sha’aban Sharaɗa da sauran jiga-jigan Jam’iyyar APC a Jihar Kano bisa zargin makircin da suke shirya masa.

Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi kakkausar suka ga gamayyar jiga-jigan Jami’iyyar APC a Jihar Kano sakamakon bita da ƙullin da yayi zargin suna shirya masa.

Tun da farko dai gamayyar fitattun Jam’iyyar ta APC a Jihar Kano ƙarƙashin Sanata Ibrahim Shekarau ne suka shirya tare da aika rubutacciyar wasiƙa zuwa ga uwar Jam’iyyar APC ta ƙasa bisa ga irin kamun ludayin Gwamna Ganduje a gudanarda Shugabancin Jihar Kano.

A cewar abinda wasiƙar ta ƙunsa; Tawagar sun bayyana cewa duk da irin gudunmawar da suka bashi shekarar 2019 wanda ya kai ga nasarar Gwamna Ganduje a Jihar Kano, a ƙarshe ya watsa musu ƙasa a ido, tare da gudanarda al’amura bisa son ransa.

A

nasa ɓangaren Gwamna Ganduje ya bayyana tawagar a matsayin gungun mutane da basu son cigaban Jam’iyyar APC a Jihar Kano, hakan shine ma ya sanya suke sukar Shugabancin Jam’iyyar wanda Abdullahi Abbas yake jagoranta.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *