• Ya Halasta Buhari ya rika amsa Sunan “President of Nigeria” a idon Doka?


Da farko, zanyi amfani da Wannan damar wurin Jajantawa al’ummar Arewa bisa Wannan musibah da ta same mu, Musamman Mutanen Sabon Birnin Jihar Sokoto, da fatar Allah ya jaddada masu Rahma, Ameeen.

•Dalilan da Suka sa bai kamata Shugaban kasa ya Cigaba da amsa Sunan “President” ba.

Gaba daya bai kamata Shugaba Buhari ya Cigaba da amsa Sunan Shugaban kasar Najeriya ba a idon Doka, domin have kundin tsarin mulkinda ya kawo shi Wannan matsayin shine kuma yace bai kamata yaci gaba da zama a matsayin Shugaban Kasar ba, don tabbatarwa mu duba Babi na biyu sashi na 14, karamin sashi na 2, (b) a cikin baka inda yace:
“Tsaron

rayuka da walwalar al’umma shine aiki na farko da ya wajaba akan gwamnati” to a duk Lokacin da gwamnati ta kasa aiwatar da aikin farko da ya wajaba a kanta, to dayan biyu ne, kodai gwamnatin nan ta sauka da kanta cikin girmamawa da mutuntawa, (Tunda ta Gaza) ko kuma Majalisar kasa ta tsige ta. Hakan zai tabbata ne dogaro da Sashi na 143 na kundin tsarin Mulkin Najeriya.

Saboda haka, Shugaban kasa:

Ya Gaza ta bangaren tsaro da tabbatar da walwala da jin dadin al’umma, (wanda hakan yasa a duniya mune Kasa ta Uku wajen ta’ddanci)
•Duba Babi Na 2, Karamin Sashi na 2 (b) a cikin baka.

Ya Gaza ta bangaren Samar da Ilimi ingantacce, (Gashinan Kullum ASUU yajin aiki take shiga, Makarantu Kullum sai kara kudi sukeyi, kayan koyo da kouarwar mu duk sun zama tsofaffin yayi)
•Duba Babi Na 2, Sashi na 18, Karamin Sashi na 3 (a, b, c, d) a cikin baka.

Ya Gaza ta bangaren Samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Kasar sa, (Kullum ‘yan Kasar sai ficewa sukeyi suna komawa wasu kasashen ketaren da suke ganin zasu dan fi samun jin dadin rayuwa)
•Duba Babi Na 2, Sashi na 16, Karamin Sashi na 1, (b) a cikin baka.

Ya Gaza ta bangaren Samar da daidaituwa wajen ayyuka da raba arzikin Kasar tsakanin yankunan guda biyu Kudu da Arewa (Ga tarin ayyuka nan ba adadi da zaka iya nunawa a kudancin Najeriya, amma ba zaka iya nuna su a arewaci ba)
•Duba Babi Na 2, Sashi na 16, Karamin Sashi na 2, (a & b) a cikin baka.

Ya Gaza ta bangaren kiwon lafiyar ‘yan Kasar sa, (Idan kaje Asibitoci Mallakin Gwamnatin tarayya zakaga yadda mutane suke mutuwa akan N2000 kacal)
•Duba Babi Na 2, Sashi Na 17, Karamin Sashi na 3 (d) a cikin baka.

Ya gaza ta bangaren Yaki da Cin hanci da rashawar da yake tinkaho (Domin kuwa yakin ana yinsa ne ga ‘Yan Adawa da kuma wasu daidaikun da suke da Matsala da gwamnatin)
•Duba Babi Na 2, Sashi Na 15, Karamin Sashi Na 5.

Ya Gaza wajen kare yaran mu da tsofaffin mu (Domin kuwa munaji muna ganin yadda ake kashe mata da kananan yara a Wannan gwamnatin amma babu wani abu da akayi.
•Duba Babi Na 2, Sashi na 17, Karamin Sashi na 3 (f) a cikin baka.

Dan haka idan muka kalla da kyau zamuga wannan gwamnatin bai kamata taci gaba da Shugabantar mu ba, kawai abinda ya kamaceta yanzu shine ta sauka da Kanta ko kuma ita Majalisa ta Kore ta (Tsigeta) dogaro da wadannan Sashen na Kundin Dokar Kasa da Wannan gwamnatin tayiwa ko take kan yiwa karan tsaye.
Ba abin kunya bane dan ya sauka a matsayin Shugaban da ya gaza, tunda ya Gaza din, anyi Shugabanni da dama da suka sauka daga kan mukaman su, sakamakon sun Gaza shawo kan matsalar tsaron Kasar su.

Allah ya bamu lafiya da zama lafiya.

Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
11th December, 2021.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *