Yanzu-Yanzu: Abdullahi Abbas ne halattaccen shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano — Uwar jam’iyyar APC ta ƙasa.

Jagorancin shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa ya nuna goyon bayansa ga tsagin Abdullahi Abbas wanda aka fi sani da ɗan sarki.

A wani hira da yayi da gidan rediyo Freedom, daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar na ƙasa, Alhaji Salisu Na inna, ya bayyana cewar, tunda dai a tsarin jam’iyyar duk ɓangaren da yake da gwamna, shine ke da jagoranci, tabbas hakan na nuna ɓangaren su Ganduje, zaɓen nasu ne karɓaɓɓe.

class="has-text-align-justify">Saboda haka, duk wani zaɓe da akayi a bisa gwadaben da bana tsarin shugaban jam’iyyar ba, hakan na nufin zaɓen ba halastacce bane.

Ya ƙara da cewa:

“Gwamna ko mai babban muƙami, idan bamu da gwamna shine gaba a jam’iyya, a duba a gani, wane zaɓe ne akayi a inda hukumar zaɓe ta turo wakilai?

“Wane zaɓe ne jami’an tsaro suka je suka tabbatar da tsaro a wajen? Don haka, wannan shine sahihin zaɓen da muka sani”.

Wannan sanarwa na zuwa kwana ɗaya da gama zaben tsagin jam’iyyar APC guda biyu da akayi jiha a Kano ne, inda jam’iyyar ta samu shugabanni har guda biyu daga ɓangaren gwamna da kuma ɓangaren tsohon Gwamna kuma sanatan Kano ta tsakiya, watau Malam Ibrahim Shekarau.

Idan za’a iya tunawa, ko a jihar Lagos, Kwara, da kuma Ogun an samu rabuwar kawuna suma.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *