YANZU-YANZU: Kotu ta rushe Shugabancin Jam’iyyar APC na Jihar Kano ta kuma bayyana tsagin Sanata Shekarau a matsayin halastacce.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Rahotanni sun tabbatar da cewa wata babbar Kotu a Abuja ta rushe zaɓen Shugabancin Jam’iyyar APC a Jihar Kano.

Babban mai shari’a CJ Hamza Muazu shine ya jagoranci shari’ar wadda mambobin Jam’iyyar ta APC tsagen Sanata Malam Ibrahim Shekarau suka shigar gabanta.

Jaridar Politics Digest ta wallafa cewar Kotun bayan rushe Shugabannin tsagin Gwamna Ganduje ta kuma ayyana ƴan takarkarun tsagin Malam Ibrahim Shekarau a matsayin waɗanda suka yi nasara.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *