Yanzu zaɓen fidda gwani ya zama sai kana da kuɗi. Delegate ko naka ne da zarar yaga daloli sai ya juya maka baya. ~Inji Sanata Kwankwaso

Jaridar Mikiya ta gano wani faifan bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta, “Inda shugaban ɗarikar Kwankwasiyya a Nigeria, Sanata Ƙwankwaso yayi zargin cewa tsarin zaɓen fidda gwani da Jam’iyyu suke gudanarwa a Nigeria ya zama sai kana da kuɗi.

Kwankwaso ya bayyanawa cewa shi yafi goyon bayan a koma tsarin da aka fara tun shekarar alif 1999, inda ake baiwa ƴan Jam’iyya masu katin Jam’iyya dama su je su zaɓi gwarzon ɗan takara a Jam’iyyarsu ma’ana ƙato-bayan-ƙato.

Har’ilyau, an hango Sanata Kwankwaso a cikin bidiyon mai tsawon mintuna 13 wanda BBC Hausa ta

wallafa yana cewa, yin amfani da tsarin “ƙato-bayan-ƙato” a zaɓen fidda gwani shi yake nuna cewa ana baiwa mutane dama su zaɓi wanda suke muradi kamar yadda yake a Demokuraɗiyance.

A ƙarshe, Sanata Kwankwaso ya shawarci Jam’iyyu akan su fidda ƴan takarkari daga yankunan da suke ganin alamun nasara, bawai yarjejeniyar yanki-yanki kamar yadda ake sharhi ba.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *