Yau za’a sanar da Shugabannin Jam’iyar APC biyu a Jihar Kano bangaren Gwamna da Kuma na ‘yan tawaye.

A wani Rahotanni da muke samu na Cewa a Yau za’a sanar da shugabannin jam’iyyar APC guda biyu a Kano, Abdullahi Abbas zai jagoranci ɓangaren gwamnati, Ɗanzago zai jagoranci APC mai jama’a ta Malam Shekarau.

Daga nan kuma sai a garzaya kotu ayi ta tafka Shari’a har kotun ƙoli.

Cikin abubuwan da ƴan APC mai jama’a ta Malam Shekarau zasu ƙalubalanci ɓangaren APC giyar mulki akwai rashin halaccin tsayawar Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyya.

Akwai doka wacce ta ce duk wani shugaba da yake sha’awar tsayawa takarar shugabanci sai ya sauka daga muƙamin sa kafin zaɓe, amma shi Abdullahi Abbas har yanzu shine ke shugabantar APCA a Kano.

Hakan

ya biyo bayan takardar koken da Wasu tawagar ‘yan majalisar dattijan Dana majalisar Tarayya Suka Kai ga uwar Jam’iyar ta APC Wanda Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya Jagoran ta bisa Rashin adalci da sukayi zargin Cewa anayi masu a Cikin Jam’iyar wata majiya ta Bayyana mana Cewa a Lokacin da su Shekarau suka Kai korafinsa Shugaban Jam’iyar na riko ya Basu wani fom Kan Cewa su Zo su jagoranci na su bangaren inyasa sai daga baya sai a kawo Shugaban rikon Jam’iyar a jihar ta kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *