Zaben 2023 mun shirya tsaf domin kwace mulki daga hannun APC ~Cewa Bukola Saraki.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya ce a yanzu Jam’iyyar PDP ta shirya kuma a shirye ta ke ta karbe ikon ta daga Jam’iyyar All Progressive Congress a 2023.

Saraki ya fadi hakan ne a taron jam’iyyar PDP na jihar Kwara da aka gudanar a cibiyar Atlantic Event center, dake Ilorin, ranar Asabar. Ya gaya wa membobin jam’iyyar su je su shirya domin cin nasarar zaben 2023.

Ya faɗawa Sabon Shugaban Jam’iyar cewa “Da zaran ka bar wannan wuri kawai aiki ya kamata ka fara Zaman lafiya na wannan Jam’iyar ya tabbatar min da cewa a shirye muke mu dawo da mulki a Kwara. ”

An

zabi membobin sabuwar jam’iyyar zartarwa ta jihar ta hanyar yarjejeniya. A karshen wannan atisaye, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Alhaji Babatunde Mohammed, ya zama shugaban Jam’iyar

A jawabinsa , sabon shugaban ya ce, “Za mu fara aiki tun daga tushe kuma za mu ci gaba da tafiya. Za mu yi amfani da kananan hukumomi don gaya wa mutanen Kwara cewa mun dawo. ”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *