Zamu koyawa Sauran Jam’iyyu mummunan Darasi a zaben 2023 Mai Zuwa.

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya ce zai koyar da sauran jam’iyyun siyasa a jihar munanan darasi ya zo 2023.

Fintiri ya bayyana haka ne a lokacin da kungiyar kansilolin jihar Adamawa ta amince da shi a dakin liyafa na gidan gwamnati da ke Yola ranar Laraba.

Gwamnan Ya Kara da Cewa “Sun gaza a cikin shekaru hudu da suka samu damar gudanar da mulki a jihar, kuma ba za mu bar su su sake yaudarar jama’armu ba, za mu ci gaba da yin aiki tukuru domjn mu samar da ribar dimokuradiyya.”

“A

kan haka, na yi imani, za mu koya musu munanan darussa cewa za su rasa dukkan zabukan daga shugaban kasa zuwa matsayi na karshe a cikin al’umma, wato na kansila,” in ji shi.
Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *