Zan biya malaman Makarantun jihata dubu talatin N30,000 mafi karancin albashi ~Cewar Gwamna zullum.

A daidai Lokacin da Rahotanni ke nuna cewa malaman makarantun jihar na fama da karancin albashi ta yadda dalibai masu shekaru 10 zuwa 15 da suka kammala aiki ke karbar Naira 13,000 duk wata.

Gwamna Babagana Zulum, a lokacin da yake kaddamar da sabuwar hukumar kula da ilimin bai daya ta jiha (SUBEB) da hukumar binciken kudi, ya ce za a yi kokarin inganta ilimi ta hanyar kara kwarin gwiwar malamai.

Ya ce, “Nagartar ilimi na raguwa saboda raunin albashi.

Za

mu tabbatar da cewa malamai akalla sun karbi mafi karancin albashi na N30,000.”

Ya bukaci SUBEB da ta aiwatar da matakan da za su tanadar da tsarin karin albashin malaman.

Ya ce kwamitoci za su zagaya makarantu a duk sassan jihar tare da gudanar da jarabawar tantancewa ga malamai domin tantance wadanda suke da cikakkiyar masaniya kan abin da ya shafi manhaja da kuma wadanda za su kara ba da horo don inganta iliminsu na sana’a.
Ya ce malaman da aka samu sun cancanta za a kara musu albashi yayin da wadanda ba su iya cika ka’idojin da ake bukata ba bayan horar da aikin yi za a mayar da su ma’aikatan da ba na ilimi ba.

Farfesa Bulama Kagu, shugaban SUBEB, ya ce hukumar za ta taka rawar gani.

A halin da ake ciki, Ibrahim Mohammed Lawallam shi ne shugaban sabuwar hukumar binciken kudi da aka kaddamar ta jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *