ZARAR BUNU: Na Rantse Da Allah Buhari Ba Zai Goyi Bayan Burin Da Tinubu Yake Dashi na Zama Shugaban Ƙasa ba – Sule Lamido

Buhari da Tinubu

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce lokacin mutuwar jam’iyyar APC ya riga daya gama zuwa, kasancewar shugaban ƙasa Muhammad Buhari ba zai goyi bayan takarar Bola Ahmed Tinubu ba a zaɓen 2023 mai zuwa.

Sule Lamido ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP na jihar Jigawa a Dutse.

Ya yi iƙirarin cewa nan gaba kaɗan za’a nemi jam’iyyar APC a rasa domin a cewar sa, ita APC an kafa ne akan mutum biyu ne, wato Buhari da Tinubu.

Gaskiyar

magana nan ba da jimawa ba, za’a nemi APC a Najeriya a rasa, saboda an kafa jam’iyyar ne akan mutane biyu, wato Buhari da Tinubu.”

Kuma na rantse da Allah, Buhari ba zai goyi bayan takarar Tinubu ba a zaben 2023 mai zuwa, ku rubuta ku ajiye”.

Don haka tunda su ne shugabannin APC kuma suna da matsala kowa zai bi hanyarsa kuma hakan ne zai zamto ƙarshen APC a Najeriya.”

Lamido, ya ce ɓallewar jam’iyyar APC ba ya nufin jam’iyyar PDP ta samu nasara sai dai idan ƴaƴan jam’iyyar sun haɗa kai.

Sule Lamido

Muna da namu matsalolin ko dai mu gyara ko kuma ƴan Najeriya za su ci gaba da shan wahala.

Dole ne mu manta da dukkan ƙorafe-ƙorafen mu, mu ajiye duk wata ɓukata ta mu domin mu samu nasara domin PDP ce kaɗai za ta iya mulkin ƙasar nan,” in ji shi.

Lamido ya bukaci mambobin kwamitin sulhun da su kasance masu adalci wajen tunkarar mambobin da suka ji haushi.

Ya kuma yi kira ga ƴan jam’iyyar da su sa jam’iyyar gaba, domin samun nasarar ta.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *