A kan batun hotunan ministan tsaro rike da bindigar AK-47 yana kokarin shiga mota, Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da martani.

A wani sako da shedikwatar tsaro ta kasa ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce labarin da ke yawo cewa an gano ministan tsaro Burgediya Janar Bashir Magashi dauke da bindigar AK-47 yana kokarin shiga mota da ita labarin karya ne.

Sanarwar ta ce wanda aka gani ajikin hoton ba Ministan tsaro bane, kuma hankalin sojojin Najeriya ya koma kan wannan gurbataccen sakon, wanda aka ƙirƙira don wulakanta Ministan tsaro.

Sanarwar ta ce “Hankalin Sojojin Najeriya ya koma kan wani gurbataccen sakon Social Media da nufin wulakanta Mai Girma Ministan Tsaro. Sojojin suna so su bayyana cewa mutumin da ke cikin bidiyon ba shine Babban Ministan Tsaro ba.”

A

makon da ya gabata ne dai wasu hotunan da aka yanko ajikin wani bidiyo sukaita yawo a Mocial Media, wadanda ake yada su ana cewa wai ministan tsaro ne ke dauke da bindigar AK-47 yayin da yake kokarin shiga mota, sai dai kuma hotunan ba su bayyana fuskar ministan ba, kasancewar ya juya baya ne yana kokarin shiga mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *