A lokutan da dama a kan saki ƴan bindigan ba tare da an yi musu shari’a ba, kuma wannan yana ƙara wa miyagun ƙrfin hali tare da kwaɗaitawa wasu su shiga aika-aikar – Gwamna Matawalle.

Gwamnan jihar Zamfara ya ce rashin hukunta ƴan bindigan da ake kamawa na cikin matsalolin da ke yin cikas wajen daƙile miyagun ayyukansu.

Kazalika ya ce akwai buƙatar a samar da kayan yaƙi irin na zamani, kafin a murƙushe ƴan bindigan da ke halaka jama’a a shiyyar Arewa maso yamma.

Gwamna Muhammad Bello matawalle na Zamfara ya yi wannan furucin ne lokacin da tawagar gwamnatin tarayya ta kai ziyarar jaje jihar dangane da kisan da ƴan bindiga suka yi wa al’ummar ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum, inda suka kashe mutane da dama a ƴan kwanakin nan.

Gwamnan

ya ce gwamnatinsa na tallafa wa jami’an tsaro da ƴan sa-kai wajen yaki da ƴan bindiga ta hanyoyi da dama, amma abin baƙin ciki shi ne yadda miyagun suke ci gaba da kai hare-hare a kan jama’a.

Sai dai ya ce sun fahimci abin da yake faruwa, “wani dalilin da ya sa wannan matsala ta ƙi ci ta ƙi cinyewa shi ne rashin hukunta miyagun da ake kamawa.

“A lokuta da dama a kan saki ƴan bindigan ba tare da an yi musu shari’a ba, kuma wannan yana ƙara wa miyagun ƙrfin hali tare da kwaɗaitawa wasu su shiga aika-aikar.

“Duk da cewa sojojinmu suna da himma, wata matsalar da muka gano ita ce rashin kayan aiki irin na zamani, kuma yaƙin zamani ba ya yiwuwa sa ida akayan aikin na zamani.

Akwai buƙatar a samar da irin waɗannan kayan faɗa na zamani idan ana so a ci nasara a wannan yaƙin a jihar Zamfara da ma shiyyar arewa maso yammacin Najeriya,” in ji shi.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *