Ainihin abin da ya faru a Lekki Toll Gate Legas.

Ainihin abin da ya faru a Lekki Toll Gate Legas shine, Sojoji sun yi amfani harsashi mara kisa, sai dai canza launin fata wajen tarwatsa masu Zanga-zanga, in ji Kukasheka.

Tsohon kakakin rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (rtd) ya ce Sojoji sun yi amfani ne da harsashin da baya kisa, sai dai sauya launin fata, wajen tarwasa masu zanga-zangar cin zarafin ‘yan sanda a Lekki Toll gate, ranar 20 ga Oktoba 2020.

A wani hira da yayi da gidan talabijin na Arise TV ranar Alhamis, Kukasheka ya ce zarge-zargen da ake yi wa Sojoji na hallaka masu Zanga-Zangan na nuna cewa “Mutane sun yanke shawarar tozarta sojoji ne tare da dora musu alhakin abinda bai faru ba amma shaidu a kasa ba sa goyon bayan wannan ikirarin”.

Tsohon

Kakakin ya Kara da cewa kamata yayi a yaba wa sojojin saboda amfani da hikima da suka yi na harba harsashin atisayi Wanda kowa ya sani bai kashe mutum.

Daga:- Aliyu Adamu Tsiga

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *