An bukaci bukaci mutanen Damaturu kada su firgita yayin da Sojoji za su tayar da bama-bamai a garin.

An nemi mazauna garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe da kewaye da kada su firgita yayin da sojoji masu yaki da injiniyoyi na hedikwata ta 2 na Operation HADIN KAI za su tayar da bama-baman da ba su tashi ba a wurare biyu a cikin babban birnin.

Wuraren su ne: kusa da jami’ar jihar Yobe a kan titin Gujba da kuma wani da ke kan titin Maiduguri.

Brig. Janar Dahiru AbdulSalam (rtd.), mai ba Gwamna Mai Mala Buni shawara na musamman kan harkokin tsaro, a ranar Talata a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Damaturu.

“An

sanar da jama’a cewa za a tada kayan fashe fashe, kuma bai kamata su firgita ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “An kuma shawarci mutane da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum saboda babu wani abin fargaba.”

“‘Yan jarida a wannan sanarwar su bada shawara ga jama’a su lura cewa ba fashewar abokan gaba ba ne, don Allah.”

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *