An kori wani Hafsan Sojan Najeriya Manjo Janar Oladipo Otiki daga aiki saboda laifin cin Amanar ƙasa.

Kotun Sojoji (Court Martial) ta zartar da hukuncin korar Manjo Janar Oladipo Otiki daga aiki sakamakon an same shi daga laifuka 5 ciki harda laifin satar kudi Naira Miliyan Dari da talatin da biyar da dubu Dari takwas, (135,800,000.

Janar Otoki shine tsohon kwamandan rundunar Sojoji ta 8 dake Jihar Sokoto, an same shi da laifin sace Miliyoyin Naira Wanda aka ware don tabbatar da tsaro a Jihar Sokoto, yanzu haka karshen aikin sa da rundunar Sojan Najeriya ya zo, an kwabe kakin sa.

Ana zargin sa da ya sace zallar kudi ne har Naira Miliyan Dari hudu, to amma an samu nasarar kwace Naira Miliyan Dari da talatin da biyar da dubu Dari takwas.

Sai da aka rage masa mukami daga Manjo Janar zuwa Birgediya Janar sannan aka kore shi bayan an kwace kudaden daya sace.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *