Babu ta yadda za’ai ace wai ƴan ta’adda sunfi ƙarfin jami’an tsaron mu — Dr Rabi’u Musa Kwankwaso

Tsohon Sanata kuma tsohon gwamnan Kano, uba ga jam’iyyar PDP ta ƙasa da Kano, ya bayyana ra’ayin sa abisa yadda al’amurran tsaro suke ta’azzara a ƙasar nan, musamman ma arewacin ƙasar.

Tsohon Sanatan ya nuna cewa, tunda yanzu dai ta kasance matsalar tsaro ta addabi kowa, lokaci yayi da za’a manta da waye ɗan PDP ko APC.

class="has-text-align-justify">A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, Kwankwaso yace, ya kyautu ace gwamnati ta samar wa sojoji kayan aiki ingantattu kuma na zamani domin yaƙi da yan ta’addan dake aikata mugun hali ga al’umma.

Kwankwaso ya kuma nuna cewa, kwata kwata yan ta’addan dake damun mutane basu da wani yawan azo agani, inda yace baya bayan nan an tura jami’an tsaro har dubu talatin jihar Anambra domin aikin zaɓe.

Kamar yadda gidan radiyon Nasara radiyo ya rawaito, Kwankwaso ya nuna cewa, tabbas jami’an tsaron Najeriya jarumai ne, domin aikin da yayi dasu a matsayin ministan tsaro, yasa ya fahimci haka.

Daga Karshe, ya zayyana cewa, da Sojojin sama, na ƙasa da ruwa, idan aka basu goyon baya da karsashi mai kyau, zasu samu nasara mai kyau akan yan ta’adda.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *