Batun DCP Abba kyari haryanzu bamu samu wasika daga FBI ta Amurka ba muma a yanar gizo muka tsinci labarin~Cewar Sufeton ‘yan sanda Usman alkali.

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ce har yanzu rundunar ‘yan sandan Najeriya ba ta samu takardar neman mika dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan kasar Abba Kyari ba Zuwa ga hukumar FBI ba tun bayan biyo bayan tuhumar da wata kotun Amurka ta yi masa.

Kamar yadda a baya MIKIYA ta ruwaito za a tunawa cewa ma’aikatar shari’a ta Amurka ta ce binciken da ake yi ya nuna cewa dan damfara ta intanet, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, ya yi zargin ya bai wa Kyari cin hanci domin ya kama wani Mai suna Kelly Chibuzo Vincent, daya daga cikin masu yi masa rakiya a Najeriya.

Hukumar

‘Yan sanda (PSC) ta dakatar da Kyari  daga ofis a matsayin Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda kuma shugaban IRT bisa shawarar IGP.

Whthing Nigeria ta ruwaito Cewa IGP Alkali Baba wanda ya bayar da karin haske kan lamarin a yau ranar Alhamis 28 ga watan Oktoba, ya ce Batun zargin da FBI takewa Abba Kyari suma sun ji ta a shafukan sada zumunta ne kawai.

Shugaban ‘yan sandan ya bayyana cewa kwamitin da aka kafa domin gudanar da bincike kan lamarin ya mika rahotonsa ga babban sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Boss Mustapha domin tantancewa da kuma ba da shawara kan binciken.

Ya kuma bayyana cewa sun samu amsa kawai daga SGF kuma suna tunanin mataki na gaba da za su ɗauka Kan Al’amarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *