Bayan an rufe layukan Sadarwa ‘Yan Bindiga sun kashe mutun sha tara 19 a karamar sabuwa ta jihar katsina.

Ranar Litinin din da ta gabata da misalin karfe 4 na asuba ‘yanta’addan daji suka kashe mutum goma Sha tara 19 a Garin Inono madawaki dake a cikin gundumar mazabar Gazari a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa dukda kullen da akasamu na hanyoyin sadarwa, har yanzu ‘yan bindiga nacin karansu ba babbaka a yankin na karamar hukumar Sabuwa dake jihar Katsina musamman ma a kauyukan su.

Bayanan dake fitowa daga wani mazaunin Garin wanda ya shigo garin Katsina da majiyar mu ta zanta da shi sun tabbatar da cewa sun kashe mutane 19 tareda raunata samada mutum 20 ta hanyar harbi da bindiga.

Wani

da yafita daga Garin yatabbatar Mana cewa maharan sun shigo Garin lokacin sallah asuba suka bude wuta Kan Mai uwa da wabi.

Karamar hukumar ta Sabuwa dai dake a kudancin jihar Katsina na cikin kananan hukumomin da matsalar tsaron ta ta’azzara. Madogarar labarin katsina Post.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *