Bayan wata da da mutuwar Shekau, Mayakan Boko Haram sun yi mubaya’a ga sabon shugaban kungiyar ISWAP.

Wasu mayakan Boko Haram sun sake hadewa da kungiyar IS a yankin Afirka ta Yamma (ISWAP), bangaren da ya balle daga kungiyar.

Wannan ci gaban na zuwa ne wata daya bayan kungiyar ISWAP ta kashe Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram.

An ce shugaban na Boko Haram ya kashe kansa ne da bam “lokacin da ya lura cewa mayakan ISWAP na son kama shi da rai”.

A wani sabon bidiyo da aka fitar ranar Asabar, an ga mayakan Boko Haram a kawance da na ISWAP.

Yayin

da suke waka cikin larabci, an ga mayakan suna dora hannayensu a kan kafadun juna.

Sun kuma yi mubaya’a ga ɗayan mayaƙan da aka ambata da suna Aba Ibrahim Al-Hashimiyil AlKhuraishi, wanda suka zaɓa tare a matsayin sabon shugabansu.

Bidiyon ya kara nuna daya daga cikin masu tayar da kayar bayan yana godiya ga sabon shugaban da ya tara su wuri daya.

Ana iya jin mai tayar da kayar bayan yana cewa duka sansanonin biyu yanzu suna cikin farin ciki da hadin kai.

Sauran mambobin kuma sun lura cewa lokaci ya yi da za a taru mu “yaƙi marasa imani”.

ISWAP ta balle daga kungiyar Boko Haram karkashin jagorancin Shekau shekaru biyar da suka gabata saboda rikicin shugabanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *