Bazan daina yin zaman sulhu da ƴan Bindigar daji ba. ~Cewar Sheikh Ahmad Gumi

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Malamin addinin Islama a Arewacin Nigeria wato Dr Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa bazai daina sulhu da ƴan Bindigar daji ba.

Gumi ya bayyana haka ne ayau Litinin yayin wata tattaunawa ta musamman tsakaninsa da wakilin TV News.

Ya bayyana cewa “mu bama son a cigaba da tsangwamar ƴan Bindigar domin yin haka zai iya sanya al’amuran su ƙara muni”.

Shehin Malamin ya kuma bayyana dalilinsa na cigaba da yin sulhu da ƴan bindigar.

Idan ba’a manta ba dai, a ranar Asabar data gaba ta ne Gwamnatin Nigeria ta ayyana ƴan Bindigar a matsayin ƴan ta’adda lamarin da Gumi yake ganin yin haka ba dai-dai bane.

class="wp-block-gallery columns-1 is-cropped">
Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *