Boko Haram ISWAD da ‘yan Bindiga ne Suka kawo karanci da tsadar Abinci a Nageriya ~Cewar Gwamnatin Buhari.

Gwamnatin tarayya ta zargi Boko Haram, ISWAP, ‘yan fashi, masu fafutukar neman kafa kasar Biafra (IPOB) da kuma ‘yan kabilar Yarbawa da karuwar karancin abinci a fadin Najeriya.

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya ce yawaitar wadannan kungiyoyi ya yi illa ga samar da abinci wanda hakan ke haifar da wani sabon salo na barazana ga kasar.

“Abin takaici, yawaitar wadannan barazanar na ci gaba da yin barazana ba kawai tsaron kasa da ci gaban tattalin arzikin kasar ba har ma da samar da abinci.

“Musamman,

samar da abinci ya yi mummunan tasiri tare da hauhawar farashin kayan abinci a fadin kasar wanda ke nuna wani sabon yanayin barazana,” in ji shi.

Mista Magashi ya bayyana haka ne a wajen bude taron masu ba da shawara ga tsaro, wanda hukumar leken asiri ta DIA ta shirya a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce hare-haren Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas da ‘yan bindiga da makiyaya a yankin Arewa maso Yamma da ta Tsakiya na kawo babbar barazana ga Najeriya.

A cewarsa, Jihohin yankin Kudu-maso-Kudu na fama da matsalar tabarbarewar man fetur ba bisa ka’ida ba, fashi da makami da kuma tsageru yayin da yankin Kudu maso Gabas ke fuskantar kalubalen neman ballewa daga kungiyar IPOB.

Ya kara da cewa yankin Kudu–maso-Yamma dai yana fuskantar yunƙurin ballewa daga masu tayar da kayar baya da kuma tashe-tashen hankula a wasu lokuta tsakanin makiyaya da manoma.

Mista Magashi ya yi kira da a hada kai tsakanin hukumomin tsaro don “fito da sabbin hanyoyin ganowa da tunkarar wadannan kalubale.

Ministan ya ce hakan ya zama dole domin “samar da yanayi mai ba da dama ga ayyukan tattalin arziki su bunƙasa da kuma jawo hannun jarin Kasashen waje kai tsaye.”

Idan baku manta ba Shugaba Buhari da Jam’iyar sa ta APC sunyi Alkawarin kawo Karshen hare-haren ta’addanci a Nageriya tun Lokacin yakin Neman zabensa na Farko 2015 da Kuma Karo na biyu a 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *