Buhari zai iya kawo karshen tada kayar baya nan da watanni 17 masu zuwa – Fadar Shugaban Kasa.

Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya ce shugabansa zai iya kawo karshen tada kayar baya kafin wa’adinsa ya kare a 2023.

Adesina ya ce gwamnatin Buhari za ta kawar da masu tayar da kayar baya nan da watanni 17 masu zuwa.

Da yake magana da gidan talabijin na Channels, mai magana da yawun shugaban kasar ya ba da labarin yadda aka kori Tamil Tigers a Sri Lanka bayan shekaru 28 na tawaye.

A cewar Adesina: “Babu abin da ba zai yiwu ba. A koyaushe ina nufin Tamil Tigers a Sri Lanka.

“Wannan

tawayen ya dau tsawon shekaru 28. Amma wata rana, an fitar da wanda ya shirya wannan tawaye, kuma shi ne ya kawo karshensa kai tsaye.

“Za a kama wadanda ke da hannu a wannan tada kayar bayan. Ana cafke su daya bayan daya kuma za a kai ga na karshensu, sannan mu kai ga karshensa. Za a iya yi a cikin watanni 17 da ya rage wa wannan gwamnati.”

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *