Da Dumi Dumi: Abu Musab Al-Barnawi shugaban ƙungiyar Boko Haram ɓangaren ISWAP ya mutu.

Kamar yadda aka sani ne, shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya mutu a bisa rigima data barke tsakanin ƙungiyoyin guda biyu wanda duk suke ikirarin cewa Boko Haramun ne.

To a yau ma, shugaban tsagin kungiyar ta Boko Haram tsagin ISWAP watau Abu Musab Al-Barnawi, ya rigamu tafiya gidan da ba’a dawowa (lahira).

Koda gidan radiyo na RFI Hausa, Saida suka ruwaito, inda suka ce, hukumar sojojin Najeriya itace ta bada wannan sanarwar. Inda suka ce:

“Ma’aikatar

tsaron Najeriya ta tabbatar da mutuwar jagoran kungiyar ISWAP Abu Musab al-Barnawi wanda cikin watan jiya, tun farko jita jita ta fara sanar da mutuwar shugaban a yayin wani fadan cikin gida tsakanin mayakan kungiyar da na Boko“.

Shin hakan na nufin ƙarshen kungiyar ne yasoma zuwa?

Bayyana ra’ayi.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *