DA DUMI-DUMI: Matasa sun yi cin-cirindo akan tituna saboda kashe-kashen da ake yi a Arewa.

A halin yanzu dai matasa na can kan titunan wasu garuruwan Arewa saboda kashe-kashen da ake yi a yankin.

Duk da cewa a halin yanzu Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro, ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda sun zafafa kai hare-hare a arewacin kasarnan duk da kokarin da gwamnati ke yi na dakile su.

An ga masu zanga-zangar dauke da alluna a jihohin Kano, Bauchi, Zamfara da Sokoto.

Suna kuma cikin Babban Birnin Tarayya (FCT)

Masu

zanga-zangar suna rera wakokin zaman lafiya, sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kara azama wajen magance matsalar rashin tsaro.

A Kano, matasan da suka nufi gidan gwamnati, suna rike da tuta mai rubutu, ‘Ba za a kara zubar da jini ba’.

Zainab Naseer Ahmad wadda ta jagoranci gangamin zaman lafiya ta koka da yadda rashin tsaro ke barazana ga rayuwar ‘yan Najeriya.

“Mun zo ne domin mu bayyana damuwarmu da aika sako ga shugabanninmu; mun gaji da tabarbarewar rashin tsaro a kasar nan.

“Kowane lokaci, ana asarar rayuka, ana kashe mutane bisa zalunci kamar dabbobi. Muna neman a dawo da zaman lafiya a cikin al’ummominmu.

“Muna cewa ya isa, ba sauran zubar da jini! Yaran da ba su zuwa makaranta suna ƙaruwa, marayu a ko’ina.

“Ba za mu iya tafiya cikin kwanciyar hankali ba, tattalin arziki yana durkushewa. Ana kona mutane yayin da suke tafiya.”

Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne daga sakatariyar Audu Bako zuwa gidan gwamnatin Kano, inda jami’an tsaro suka tarbi gungun masu zanga-zangar, suka saurare su tare da yi musu alkawarin za su mika kukansu zuwa inda ya dace.

An dai nuna bacin rai a kasar tun bayan da ‘yan bindiga suka kona wasu matafiya da ransu a Sokoto a farkon makon nan.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *