Da Dumi Dumi: ‘Yan bindiga sun kai hari a Makarantar Cocin Kiristoci ta Katolika da ke Kaduna, sun yi garkuwa da adadi mai yawa.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargi’ yan fashi ne sun kai hari kan St. Albert the Great Institute of Philosophy, makarantar hauza ta Cocin Katolika.

Makarantar karatun tana cikin garin Fayit, Kagoma Masarautar Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna.

Harin kamar yadda rahotanni suka bayyana ya kai ga sace daliban da ba a bayyana adadinsu ba.

Lamarin ya faru ne a daren Litinin lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye harabar makarantar, suna ta harbe -harbe kafin daga bisani su tafi da wadanda abin ya shafa.

Da

aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ya ce har yanzu bai samu rahoton ba.

PPRO din ya ce “zai tuntubi jami’an tsaron yankin sannan ya dawo” ga wakilin mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *